An kashe mutane 25 a wasu sabbin hare-hare a Benue

46

Akalla mutane 25 ne aka kashe a hare-haren da aka kai wasu kauyukan kananan hukumomi uku na jihar Benue da safiyar yau.

An bayyana cewa, kauyukan da ke kananan hukumomi uku na Guma, Logo da Tarka sun sha fama da harbe-harbe daga karfe 8 zuwa 3 na dare a jiya, a wani hari da wasu mahara suka kai.

An gano gawarwaki 15 a wani kauye da ke karamar hukumar Tarka yayin da aka gano wasu 9 a Guma sai kuma gawar wani basarake a Logo.

Mazauna kauyukan sun ce adadin gawarwakin na iya karuwa saboda ana cigaba da neman wadanda suka bace a lokacin da ake gabatar da wannan rahoton.

Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, ya tabbatar wa manema labarai cewa an kashe mutane bakwai a wani hari da aka yi kan wani kauye a karamar hukumar Guma.

Mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin tsaro Paul Hemba, ya ce adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu zai iya haura 25 kasancewar ana cigaba da neman wadanda suka bata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × three =