NDA ta yaye dalibai 295 zuwa cikakken sojoji

69

Makarantar horas da sojoji ta kasa ta yaye dalibai 295 na gajeren kwas karo na 47 zuwa rundunar sojojin Najeriya yau a Kaduna.

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, shi ne jami’in bita a wajen bikin kaddamar da sabbin jami’an.

Ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyansu su yi koyi aiki da sauri da kuma dacewa da yanayin aikinsu, yana mai cewa cigaban sana’arsu zai dogara ne kan halayensu da kokarinsu na cigaban kansu.

Ministan ya hori sabbin jami’an da su tsare martaba da kare kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya tare da yi wa kasa hidima ba tare da son kai ba, cikin aminci da gaskiya.

Ya ce rundunar soji da sauran hukumomin leken asiri da na tsaro za su cigaba da dogaro da goyon bayan dukkanin ‘yan Najeriya a kokarin hadin gwiwa na tinkarar duk wata barazana ga tsaron kasa.

Bashir Magashi ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa jajircewa da kokarinsa wajen inganta tsaro da cigaban kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + six =