Lawan ya yi kira ga sojoji su kare ‘yan Najeriya

72

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya bukaci sojoji da su tashi tsaye tare da kare ‘yan Najeriya.

Ya yi rokon bayan daya daga cikin abokan aikinsa ya gabatar da kudiri akan bukatar gaggawa da ake da ita ta daukar tsauraran matakan kawo karshen ‘yan fashin daji da garkuwa da mutane.

Da yake magana a zauren majalisar a yau, Sanata Bello Mandiya daga Katsina ta Kudu yace matsalar ‘yan fashin daji da garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a jihar Katsina.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakan dakile matsalar ta hanyar kafa operation sharan daji da tawagar tsaro ta hadin gwiwa domin dakile fashin daji, satar shanu da garkuwa da mutane.

Da yake bayar da gudunmawa akan kudirin, Sanata Kabir Abdullahi Barkiya, daga Katsina ta tsakiya, ya koka dangane da gazawar sojoji na shawo kan matsalar duk da kiraye-kirayen da aka yi musu na su dauki mataki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty + 14 =