Za a kammala tashar wutar lantarki ta Zungeru a bana

58

Kamfanin Sino Hydro dake kwangilar aikin tashar wutar lantarki ta Zungeru ya bayar da tabbacin cewa za a kaddamar da aikin wutar lantarkin mai karfin megawata 700 cikin rukunoni 4 a bana.

Wata sanarwa daga mataimakin manajan ayyukan kamfanin tace a watanni ukun farko na bana za a kaddamar da rukuni na farko na tashar da zai samar da megawatt 175.

A cewarsa, ana sa ran kaddamar da rukuni na biyu na tashar da zai samar da megawatt 175 a tsakiyar bana, yayin da za a kaddamar da rukuni na uku cikin watanni taran bana, kuma za a kaddamar da rukuni na hudu a watan Disambar bana.

Idan za a iya tunawa dai tashar wutar lantarki ta Zungure da kamfanin Sino Hydro yake ginawa a jihar Neja zata samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 700.

Tashar ta Zungeru zata zama tashar wutar lantarki ta biyu mafi girma a kasarnan, bayan tashar Kainji mai karfin megawatt 760.

Tashar na daya daga cikin manyan tashoshin wuta mafiya girma a Afirka wacce gwamnati ta ciyo bashi daga bankin Exim na kasar China domin ginawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 − 6 =