An kashe mutum daya a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

74

Rundunar yansandan jihar Jigawa ta tabbatar da kisan wani mutum guda wanda aka samu gawarsa a cikin daji yayin fada tsakanin makiyaya da manoma a jihar Jigawa.

Hakan na zuwa ne bayan wasu shaidun gani da ido sun ce akalla mutane 12 aka kashe yayin rikicin wanda ya auku a garuruwan Matarar Gamji da Madachi, dake yankin karamar hukumar Kirikasamma.

An rawaito cewa fadan ya fara ne yayin da makiyayan tare da shanunsu aka yi zargin sun mamaye gonaki tare da lalata amfanin gona a garuruwan biyu.

Wani da ya shaida rikicin da idonsa, Idris Madachi, ya gayawa manema labarai cewa makiyayan tare da shanunsu sun mamaye gonaki tare da lalata amfanin gona kuma hakan ya bakantawa manoman rai.

Da aka nemi jin ta bakinsa, kakakin yansandan jiha, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A wani labarin kuma, ‘yansanda a jihar Jigawa sun kama wani malamin makaranta mai shekara 38 bisa zargin sace dalibarsa da yi mata fyade a yankin karamar hukumar Dutse.

Kakakin rundunar yansandan jiha, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa ga manema labarai.

Wanda ake zargin, wanda malamin makaranta ne a makarantar sakandiren gwamnati ta jeka ka dawo a Wurno, ya dauke dalibarsa daga kauyen Wurno zuwa wani gida a birnin Dutse, inda ya kwana da ita tare da yi mata fyade.

An kai malamin da dalibar zuwa cibiyar da ake kai wadanda aka yiwa fyade a babban asibitin Dutse domin duba lafiyarsu.

Shiisu Adam yace a lokacin da ake bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

Yace har yanzu ana cigaba da bincike kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight − 2 =