Wata zaftarewar kasa a wani wajen gine-gine a lardin kudu maso yammacin kasar China ta kashe akalla mutane 14.
Kafar yada labaran gwamnati a yau ta bayar da rahoton cewa ma’aikata na tsaka da aiki lokacin da zaftarewar kasar ta auku a jiya da yamma.
Masu aikin ceto sun samu gawarwaki 14 tare da wasu mutane 3 da suka samu raunuka, kuma ana cigaba da binciken musabbabin hatsarin.
Ana yawan samun hatsari a wajen gine-gine da masana’antu a kasar ta China.
Ko a watan Disambar da ya gabata, ma’aikata biyu sun mutu yayin da aka ceto wasu 20 daga wani wajen hakar kwal.
A watan Yulin bara, ma’aikata 14 sun mutu a wani lardin kudancin China bayan wani bututu da suke ginawa ya cika da ruwa.