Jami’an tsaro a kasar Sudan sun harba hayaki mai sa hawaye a kokarin tarwatsa zanga-zangar neman demokradiyya a babban birnin kasar Khartoum da birnin Port Sudan.
Mutane a birane dayawa na rera wakokin kin jinin sojoji tare da kiran a rushe majalisar mulkin Sudan.
Majalisar na karkashin mulkin Janar Abdel Fatah al-Burhan wanda ya jagorancin juyin mulkin sojoji a watan Oktaban bara.
A birnin Omdurman dake makotaka da Khartoum, gomman mutane sun kafa shingen ababen hawa.
Zanga-zangar na zuwa ne kwanaki 2 bayan murabus din fira-ministan kasar na farar hula, Abdalla Hamdok.
Mutane 56 ne suka mutu a jerin zanga-zanga tun daga juyin mulkin na watan Oktoba, dayawansu jami’an tsaro ne suka harbe su.
A baya an bayar da rahoton cewa an aika da jami’an tsaron Sudan zuwa sassan babban birnin kasar, Khartoum, da sauran birane, gabannin zanga-zangar.