Gwamnatin Tarayya tana shirin kara wa’adin fara aiwatar da cire tallafin man fetur da watanni 18.
Karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya sanar da haka a yau lokacin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa a Abuja.
Ya sanar da cewa gwamnati ta kammala shirye-shiryen tunkarar majalisun kasa domin neman gyara dokar man fetur ta PIA.
Timipre Sylva, wanda yake shugabantar kwamitin fara aiwatar da dokar ta PIA, ya jaddada cewa matakin bangaren gwamnati na neman gyara dokar, ba shi da alaka da siyasa.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 16 ga watan Augustan 2021, ya sanya hannu akan dokar man fetur ta PIA.