Cin hanci da rashawa ya kara muni a Najeriya

3

Najeriya ta kara yiwowa kasa a sakamakon binciken cin hanci da rashawa wanda kungiyar Transparency International ta wallafa.

A sakamakon na shekarar 2021 wanda kungiyar ta fitar a yau, Najeriya ta yi kasa da mataki 5.

Kasarnan ta samu maki 24 daga cikin 100, inda ta zama kasa ta 154 cikin 180 a bangaren cin hanci da rashawa.

Wannan ce shekara ta biyu a jere da Najeriya ke samun koma baya a sakamakon yaki da cin hanci da rashawa. Makin kasarnan ya ragu daga 26 a shekarar 2019 zuwa 25 a shekarar 2020, inda ya kara raguwa zuwa 24 a sakamakon baya-bayanan na 2021.

Kazalika a shafinta na internet, kungiyar Transparency International ta yi bayanin cewa wannan shine maki mafi karanci da Najeriya ta samu a sakamakon yaki da cin hanci da rashawa.

Kungiyar Transparency International ce ke fitar da sakamakon domin auna matakin cin hanci da rashawa na kasashen duniya daban-daban. Maki mafi yawa da kasa za ta iya samu shine 100, mafi karanci kuma shine sifili.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − sixteen =