Ban gamsu da kafa ‘yansandan jihohi ba – Buhari

14

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi amannar cewa tsarin ‘yansandan jihoshi ba shi zai haifar da da mai ido ba ga kasarnan.

Shugaban kasar ya sanar da haka a wata fira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.

Shugaban kasar ya kare matsayarsa da cewa akwai yiwuwar gwamnoni suyi amfani da yansandan jihoshi wajen cimma burinsu na siyasa.

Da yake magana akan yanayin tsaro a kasarnan, shugaban kasar yace dole sarakunan gargajiya su taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya a kauyukansu.

Ya kuma bukaci karin tattaunawa wajen magance rikicin manoma da makiyaya da ake samu a kasarnan.

A wani batun kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Magaret Chuba Okadigbo a matsayin shugabar kwamitin gudanarwar kamfanin man fetur na kasa (NNPC).

Magaret Okadigbo ta maye gurbin Ifeanyi Ararume, wanda shugaban kasar ya nada lokacin da aka kaddamar da kwamitin a ranar 19 ga watan Satumbar bara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + 15 =