Babu mai laifin da zai tsira saboda ya shiga APC – Buhari

21

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu wanda ake zargi da cin hanci da rashawa da zai iya tsira koda kuwa ya koma jam’iyyarsa ta APC.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da gidan talabijin na NTA a jiya.

‘Yan Najeriya dai na ganin cewa ‘yan jam’iyyun adawa da ake zargi da cin hanci da rashawa suna shiga jam’iyyar APC ne domin gudun kada a hukunta su.

Wasu ‘yan siyasa da ake zargi da cin hanci da rashawa da suka koma jam’iyya mai mulki sun hada da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da kuma ‘yar majalisar dattawa, Stella Oduah.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi iya kokarinsa ga kasar, kuma yana fatan ‘yan Najeriya za su yi tuna baya tare da fahimtar kokarinsa bayan ya bar mulki.

Da yake jawabi yayin hirar, shugaba Buhari ya ce ba ya bukatar godiya daga ‘yan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + 2 =