Jami’an tsaro a kasar Kazakhstan sun ce sun kashe masu zanga-zangar adawa da gwamnati da dama a wani samame da suke yi na dawo da zaman lafiya a babban birnin kasar, Almaty.
Wata mai magana da yawun ‘yan sandan ta ce a yau ne hukumomi suka dakile mutane da dama a lokacin da suka yi kokarin kutsawa cikin gine-ginen gwamnati, da hedikwatar ‘yan sanda, da ofisoshin ‘yan sanda na gundumomi.
Kimanin mutane dubu 1 ne aka ruwaito sun jikkata a rikicin, inda 400 ke jinya a asibiti, 62 kuma na cikin tsananin kulawa.
Rundunar ‘yan sandan ta ce masu zanga-zangar sun kona motoci 120 da suka hada da na ‘yan sanda 33, tare da lalata shagunan kasuwanci kimanin 400, sannan an tsare mutane sama da 200.
An fara zanga-zangar lami lafiya ranar Lahadi bayan da gwamnati ta ninka kudin man fetur.
Bayan rashin gamsuwa da sanarwar murabus din gwamnati a jiya da safe, masu zanga-zangar sun karbe iko da babban filin jirgin saman kasar.