Yansanda sun kashe ‘yan fashin daji 2 a Kaduna

13

‘Yan sandan Jihar Kaduna sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga biyu da suka addabi yankin Karamar Hukumar Giwa yayin wata arangama.

Dakarun rundunar ta 47 dake Zariya ne suka gamu da ‘yan fashin yayin da suke kan aikin sintiri a kusa da kauyen Riheyi na garin Fatika jiya da dare, in ji kakakin rundunar a Kaduna Mohammed Jalige.

Da yake magana da manema labarai, Jalige ya ce nan take suka fara fafatawa, inda jami’ansu suka yi nasarar kashe biyu daga cikinsu.

Ya kara da cewa ‘yan sanda sun kwace bindiagar AK-47 da kuma harsasai daga hannun ‘yan fashin.

A wani labarin kuma, an kashe mutane da dama tare da sace wasu yayin da ‘yan fashi suka bude wa matafiya wuta a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya jiya da dare.

An ruwaito cewa maharan sun fara harbe-harben ne a daidai garin Kofar Gayan da ke kusa da birnin Zariya da misalin ƙarfe 8 na dare.

Wasu da suka shaida lamarin sun bayyanawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi don su tashi hankalin matafiyan da zimmar yin garkuwa da su.

A cewar shaidun, hakan ya sa suka yi awon gaba da wasu zuwa cikin daji kafin isowar jami’an tsaro.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − 9 =