Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 27 bisa laifin fashi da makami da garkuwa da mutane.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, jiya a Dutse.
Shiisu Lawan ya ce, tawagar ‘yan sandan da ke aiki a Ringim ne suka kama wanda ake zargin.
Ya bayyana cewa ana kyautata zaton wanda ake zargin dan wani gungun ‘yan fashine da suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim Jinjiri mai shekaru 60 a kauyen Zangon Kanya da ke karamar hukumar Ringim a watan Satumbar bara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ya tunatar da cewa gungun sun yi garkuwa da wanda abin ya shafa bayan sun yi masa fashin naira dubu 300.
A cewar Shiisu Lawan, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.
A wani cigaban kuma, Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai shekaru 40 da haihuwa bisa zargin satar motar daukar marasa lafiya ta karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar jiya a Dutse.
Shiisu Adam ya ce an kama wanda ake zargin ne a kauyen Takwasa da ke karamar hukumar Babura a jiharnan.
Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne bayan da ‘yan sanda suka samu rahoton cewa an sace motar daukar marasa lafiya a kauyen Kanya Hore da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan ya ce ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin bayan an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.