Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Buni-Yadi

29

Sojojin Najeriya sun dakile yunkurin mayakan Boko Haram da na ISWAP na kai hari jiya a garin Buni-Yadi da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

An yi ta shewa a garin yayin da mazauna garin suka yi ta murna tare da yaba wa sojojin Najeriya da suka fatattaki mayakan.

An rawaito cewa sojojin kasa sun yi artabu da mayakan, yayin da jiragen yakin sojojin saman Najeriya suka yi ruwan bama-bamai a kan mayakan da ke tahowa zuwa Buni-Yadi a cikin wata motar yaki.

Wani manomin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun ga mayakan na Boko Haram na yunkurin tsallaka rafi da motocinsu.

Hakazalika wata majiyar tsaro ta tabbatar da nasarar da aka samu a kan mayakan, inda ta ce an kwace motocinsu na yaki tare da kashe mayakan Boko Haram da dama.

A cewar rahoton PRNigeria, rundunar sojoji na musamman da rundunar sojin saman Najeriya sun dakile harin da aka kai a makarantar sojoji na musamman da ke Buni-Yadi a Jihar Yobe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × five =