Gwamna Masari ya nemi mazauna Katsina su kare kawunansu

17

Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta dage haramcin toshe hanyoyin sadarwa a sauran kananan hukumomi bakwai da lamarin ya shafa kafin watan Janairu mai zuwa.

Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai jiya a Katsina, ya bukaci mazauna yankin da su yi iya kokarinsu wajen kare yankunansu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Ya yabawa kokarin dukkanin hukumomin tsaro musamman kungiyoyin ‘yan banga wajen yaki da ‘yan bindiga.

Gwamna Masari ya bayyana cewa ’yan banga na tafiya daga wannan kauyen zuwa waccan da nufin kare al’umma.

Gwamnan ya kuma shawarci jama’a da su kare al’ummarsu tare da baiwa jami’an tsaro duk wani tallafi da ya kamata, musamman ta hanyar basu sahihin bayanai kan masu aikata laifuka.

Gwamnan ya bukaci al’ummar da ke cikin kauyuka daban-daban da su tallafa wa kungiyoyin ‘yan sa-kai na yankin da makaman da suka dace domin su kare su idan aka kai musu hari.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 − 4 =