Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada bukatar shugabannin kasashen Afirka su hada karfi da karfe domin dakile ayyukan ta’addanci a nahiyar.
Ya bayyana hakan ne a jiya a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar domin jajantawa al’ummar kasa da shugaban kasar jamhuriyar Nijar Mohammed Bazoum kan kisan mutane 69 da ‘yan tawaye suka yi a kan iyakar kasar da Mali da Burkina Faso.
Shugaban kasar wanda ya bayyana matukar kaduwarsa da alhininsa kan lamarin, ya ce cin zarafi da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, barazana ce a ko’ina a nahiyar Afirka, don haka akwai bukatar gaggawar kara hada kai a tsakanin kasashen Afirka wajen kawar da barazanar ta’addanci.
Ya kara da cewa wannan mummunan harin da aka kai kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da wani magajin gari a Jamhuriyar Nijar, wani koma baya ne ga kokarin da yankin ke yi na dakile ayyukan ta’addanci.
A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su ke bayar da goyon baya ga kayayyakin da ake samarwa a cikin kasa domin habaka harkokin kasuwanci da damarmaki a kasarnan.
Ya fadi hakan haka a jiya a jawabinsa wajen bude bikin bajekoli na duniya karo na 35 a Lagos, wanda cibiyar kasuwanci da masana’antu ta Lagos ta shirya.
Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan masana’antu, cinikayya da zuba jari, Otunba Niyi Adebayo, ya bayyana kasuwanci a matsayin ginshikin kawo karshen talauci, da inganta rayuwar mutane, da habaka cigaban tattalin arziki.
Shugaban kasar ya sanar da cewa daya daga cikin manyan kudirorin gwamnatin tarayya shine samar da yanayin da zai bunkasa kasuwanni.
Shugabar cibiyar, Toki Mabogunje, a jawabinta na maraba, tace shirye-shiryen cibiyar da harkokinta da horas da ma’aikata, ana gudanar da su ne domin habaka tattalin arziki.