Buhari yana ganawa da shugabannin tsaro

10

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar tsaron kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda suke halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Leo Irabor.

Hafsan hafsoshin soji uku da na ruwa da na sama da na kasa da kuma sufeto janar na ‘yan sanda Usman Alkali Baba suna halartar taron.

An bayyana cewa taron zai sake baiwa shugaban kasar damar samun karin bayani kan al’amuran tsaro na baya-bayan nan a kasarnan.

Shugaba Buhari tare da taimakon mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yi wa dogarinsa Laftanar Kanar Yusuf Mukhtar Dodo karin girma na Kanar kafin a fara taron.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × three =