Buhari ya bayar da umarnin tsare hanyar Abuja-Kaduna

18

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron kasarnan da su kawar da barazanar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna da sauran wurare a fadin kasarnan.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a jiya a karshen taron kwamitin tsaro na kasa da shugaban kasar ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda suke halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Leo Irabor.

Hafsan hafsoshin soji uku da na ruwa da na sama da na kasa da kuma sufeto janar na ‘yan sanda Usman Alkali Baba suna halartar taron.

Aregbesola ya ce shugaban kasar ya umarci jami’an tsaro da sauran hukumomin tsaro da kungiyoyin leken asiri da kada su yi kasa a gwiwa, duk kuwa da irin cigaba da kokarin da ake yi na kawar da ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da sauran masu aikata miyagun laifuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 + 4 =