Yansanda sun karyata shirin dawo da SARS

41

Rundunar ‘yansandan kasa tace bata da wani shiri na dawo da tawagar yansanda ta musamman ta SARS wacce aka rushe.

Kakakin rundunar yansandan kasa, Frank Mba, ya sanar da haka cikin wata sanarwa jiya a Abuja.

Sanarwar tazo ne daidai lokacin da ake ta yada jita-jita, musamman a kafafen sadarwa, cewa rundunar ‘yansanda na shirin dawo da tsohuwar tawagar.

Sufeto Janar na yansanda na baya, Mohammed Adamu, a bara ya sanar da rushe tawagar wacce aka kyama.

Rushe tawagar yazo ne bayan dubban ‘yan Najeriya, musamman matasa, sun bazama kan tituna suna zanga-zangar cin zarafin da jami’an tawagar ke yi.

Biyo bayan rushe tawagar, rundunar yansanda ta kirkiri sabuwar tawaga mai suna SWAT wacce zata maye gurbinta.

Cikin sanarwar, Frank Mba, ya bukaci ‘yan Najeriya da su watsi da rade-radin, inda yace tsohuwar tawagar ta tafi kenan har abada.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × three =