Najeriya na cikin lokaci mafi kalubale a tarihinta – Buhari

46

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa watanni 18 da suka gabata sune mafi kalubale a tarihin Najeriya.

Shugaban kasar ya fadi haka ne yau yayin watsa jawabinsa ta gidan talabijin don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Kalaman na shugaban na zuwa ne a yayin da kusan dukkan sassan Najeriya ke fama da wani nau’i na aikata laifuka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki a shekarar 2015 bisa alkawarin da ya dauka na magance matsalar rashin tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da inganta tattalin arziki.

A wani labarin makamancin wannnan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa wani dan majalisar wakilai yana daga cikin wadanda ke tallafa wa ‘yan aware a kasarnan.

Shugaban ya ce kamen da aka yi wa Nnamdi Kanu da Sunday Igboho kwanannan ya bayyana manyan mutane dake daukar nauyinsu, da suka hada da dan majalisar.

Sai dai bai bayyana sunan dan majalisar ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − eleven =