MDD tace akwai fatan komai zai daidaita a Arewa maso Gabas

22

Majalisar Dinkin Duniya ta ce da alama akwai kyakykyawan fatan komai zai dawo daidai cikin shekaru kadan masu zuwa a yankin Arewa maso Gabas.

Da take yi wa manema labarai jawabi jiya a Abuja, Mai Taimakawa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ahunna Eziakonwa, ta ce an samu gagarumin ci gaba a yankin.

Eziakonwa wacce kuma ita ce Daraktar Yankin Afrika ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tallafin da Majalisar Dinkin Duniya ke bayarwa ya riga ya kawo gagarumin cigaba.

Eziakonwa wacce tazo Najeriya a ziyarar aiki don samun damar duba sakamakon tallafin Majalisar Dinkin Duniya, duk da haka, tace akwai sauran aiki da yawa da za a yi nan gaba.

Ta bayyana aikin ta a matsayin mai cike da damuwa, kasancewar an haife ta kuma ta girma a Najeriya.

Eziakonwa ta yi nuni da cewa makarantu sun dawo tare da malaman da ke aiki ba tare da matsala ba a kauyukan yankin.

A wani labarin kuma, ofishin shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a tilasta masa rage rabon abinci ga mata da maza da yara sama da rabin miliyan a Arewa maso Gabas.

Daraktan Shirin na Yammacin Afirka, Chris Nikoi ya fadi hakan cikin wata sanarwa yau a Abuja, bayan wata ziyara da ya kawo Najeriya kwanannan.

Ya ce shirin zai yi haka ne muddin ba a samu tallafin gaggawa ba, domin cigaba da ayyukan ceton rayuka a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Daraktan ya bayyana cewa ragin zai zo daidai lokacin da ake fama matsananciyar yunwa mafi muni cikin shekaru biyar a kasarnan, sakamakon rikice-rikice da rashin tsaro.

Ya ce lamarin ya kara ta’azzara sakamakon tabarbarewar zamantakewa da tattalin arziki sanadiyyar annobar corona da hauhawar farashin kayan abinci da kuma karancin abincin.

Ya kara da cewa adadin mutanen da suka rasa muhallansu ya haura miliyan biyu zuwa watan Satumbar da ya gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − 15 =