Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Lucky Irabor, yace hukumomin tsaro ya zuwa yanzu sun kashe ‘yan fashin daji 250 tare da kame sama da 600 tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara da wasu bangarorin jihoshin Neja da Sokoto da Kaduna.
Lucky Irabor ya sanar da haka a wajen dawowar taron bayyana ayyukan ministoci wanda tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya, karkashin jagorancin Femi Adesina, jiya a Abuja.
Lucky Irabor ya kuma sanar da cewa an ceto dubban mutanen da aka sace daga sansanoni daban-daban na ‘yan fashin daji dake jihoshin Zamfara da Sokoto da Katsina, cikin makonni 5 da suka gabata.
Ya jaddada jajircewar sojoji na cigaba da yakar ‘yan fashin daji da sauran batagari dake addabar wasu sassan kasarnan.
Da yake tsokaci dangane da mika wuyar da yan Boko Haram suke yi a ‘yan kwanakinnan, Lucky Irabor yace mayaka sama da dubu 1 da 800 ne kawo yanzu suka mika wuya.
Yayi kira ga masu ruwa da tsaki da dukkan ‘yan kasa da su hada kai da hukumomin tsaro domin samun nasarar yakin da ake yi da ta’addanci.