Bazan huta ba har sai Najeriya da fita daga matsalar rashin tsaro – Buhari

19

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa baza tayi kasa a gwiwa ba har sai an magance kalubalen tsaro da ake fuskantar a kasarnan.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu, ya fadi haka a wajen bikin kaddamar da wani littafi wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta, da aka gudanar a Abuja.

Yace gwamnatin tana assasa hadin kai tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro domin aiki tare wajen yaki da aikata laifuka da sauran ayyukan ashsha a kasarnan.

Shugaba Buhari yace an samar da isassun kudade da kayan aiki domin karfafa sojoji da nufin inganta ayyukansu.

Ya yabawa dakarun sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa kokarinsu na yakar aikata laifuka da sauran ayyukan ashsha a kasarnan.

Ya jaddada cewa tilas a samu nasara a yaki da rashin tsaro, inda yace dole Najeriya ta zauna lafiya kuma ‘yan Najeriya suyi rayuwa cikin lumana da tsaro.

A wani cigaban mai alaka da wannan, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hori shugabannin yankin Ogoni da ‘yan asalin yankin dangane da muhimmanci tsare kadarorin kasa irinsu bututun mai da sauran kayayyakin hakar mai.

Shugaban kasar, wanda ya fadi haka a yau lokacin da ya karbi bakuncin shugabanni da mutanen yankin Ogoni a fadar shugaban kasa dake Abuja, yayi nuni da cewa lalata kadarorin yana kara bata musu muhalli da dakile cigaba a yankin.

Yace gwamnatin tarayya tana da aniyar share dagwalon mai na yankin Ogoni saboda ‘yan asalin yankin su koma rayuwarsu ta asali da sake komawa gonaki wanda zai farfado da harkokin tattalin arziki.

Shugaban kasar yace ayyukan da basu dace ba na kamfanonin mai hade da kalubalen tsaro ne suka jawo kwararar mai da lalata muhalli a yankin Ogoni, lamarin da haifar da rigingimu a kotuna da zanga-zanga.

Yace gwamnati zata mayar da hankali kan dukkan bukatun mutanen yankin Ogoni.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 1 =