Majalisa ta bukaci Buhari ya ayyana ‘yan fashi a matsayin ‘yan ta’adda

106

Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ‘yan fashin dajin da suka addabi yankin arewacin kasarnan a matsayin ‘yan ta’adda, tare da ayyana yaki a kansu.

Majalisar ta kuma bukaci a shafe su daga doron duniya ta hanyar fara tarwatsa wuraren fakewarsu da jefa musu bama-bamai.

‘Yan Majalisar Dattawan na kuma son shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shugabannin ‘yan fashin dajin a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo, domin kamo su a hukunta su.

An amince da wannan matsaya ne bayan wani kuduri da daya daga cikin ‘yan majalisar Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya gabatar da hadin guiwar wasu takwarorinsa takwas.

Abdullahi Gobir yayi nuni da cewa majalisar dan majalisar dattawa ta Sokoto ta zama mafakar ‘yan fashin daji saboda fatattakarsu da ake yi a jihar Zamfara.

Ya tunatar da kisan da ‘yan bindigar suka yiwa jami’an tsaro 21 da aka yi a kauyukan Dama da Gangara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 − 7 =