Gwamnatin jihar Kaduna ta katse layukan sadarwa

108

Gwamnatin jihar Kaduna ta ba da umarnin rufe ayyukan sadarwa don magance kwararar ‘yan bindiga daga jihohin Zamfara da Katsina.

Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya sake nanata sanarwar da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna da safiyar yau, ya kuma sanar da haramta dukkan amfani da babura a fadin jihar na tsawon watanni uku.

A cewar Samuel Aruwan, tuni hukumomin tarayya da abin ya shafa suka sanar da Gwamnatin Jihar cewa an fara shirye -shiryen rufe hanyoyin sadarwa a sassan jihar.

An rawaito Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da al’ummar jiharsa cewa su shirya domin za a katse layukan sadarwa a kokarin da jami’an tsaro ke yi na kaddamar da hari kan ‘yan bindiga da ke buya a wasu kananan hukumomi.

Gwamna El-Rufai ya ce katse layukan ba zai shafi duk jihar ba, amma wasu sassan na jihar kamar kananan hukumomin da ke iyaka da Zamfara da Katsina za a katse layukansu.

El-Rufai ya ce katse layukan da aka yi a jihohin Zamfara da Katsina ya bai wa ‘yan bindiga damar kutsa kai wasu kauyukan makwabtan jihohi kamar Kaduna domin amfani da layukan waya don amsar kudin fansa.

Ya kara da cewa tuni ya aike wa gwamnatin tarayya wannan bukata wanda ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da matakin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + 2 =