‘Yan bindiga sun kai hari makarantar sojoji ta NDA a Kaduna

60

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta NDA da ke Afaka a Kaduna.

Wasu shaidun gani da ido, sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace guda daya yayin harin da suka kai jiya da tsakar dare.

Sanarwar da mai magana da yawun Makarantar Sojojin, Manjo Bashir Muhammad Jajira, ya fitar daga bisani ta tabbatar da kai harin.

Ya ce ‘yan bindigar sun shiga bangaren gidaje na Makarantar inda suka kai hari lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’ansu biyu sannan aka sace guda daya.

Ya kara da cewa jami’an tsaro sun soma bin bayan ‘yan bindigar da zummar far musu da kuma ceto mutumin da aka sace.

An bude reshen sabuwar makarantar ta NDA a Afaka a watan Fabrairu 2007. Inda tsohuwar makarantar dake cikin Kaduna ta zama ta masu karatun digiri na biyu zuwa sama.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + 12 =