Kamfanin KEDCO ya gargadi abokan hulda bisa tsallaken mita

18

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki KEDCO ya ce kamfanin yana yin asarar kudaden shiga sakamakon tsallaken mita da jan wuta ta haramtacciyar hanya a Jihohin Jigawa, Kano da Katsina.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban Sadarwa na KEDCO, Ibrahim Sani-Shawai, da ya fitar yau a Kano.

Kamfanin ya ce abokan huldarsa sama da 17,190 dake amfani da mita, basu sayi kati ba, tsakanin watan Janairu zuwa Yulin da ya gabata.

Sani-Shawai ya ce bisa tanadin dokokin aiki, duk wanda aka kama yana tsallaken mita za a yi masa hukunci gwargwadon nauyin laifin da ya aikata.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu taka tsantsan don tabbatar da cewa ba a taba mitar su ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 7 =