Ana fargabar mutuwar mutane 52 bayan jirgin ruwa ya kife a Sifaniya

146

Fiye da mutane 50 ake fargabar sun mutu bayan da wani jirgin ruwa ya kife a tekun Atlantika kimanin kilomita 220 daga tsibirran Canary na Sifaniya.

Hukumar ceton ruwa ta Sifaniya ta ce wata mata ‘yar shekara 30 ce kadai ta tsira a jiya daga jirgin ruwan da ya nutse, wanda ya bar Afirka mako guda da ya gabata dauke da bakin haure da ‘yan gudun hijira su 53.

Wani jami’in hukumar ceto, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa matar tana rike da jikin jirgin da ke nutsewa a tsakiyar wasu gawarwaki biyu.

Ta shaidawa masu aikin ceto cewa jirgin ruwan dake amfani da iska, ya taso ne daga gabar yammacin Sahara kuma fasinjojinsa sun fito ne daga kasar Ivory Coast.

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, akalla mutane 250 ne suka mutu a hanyarsu ta zuwa Sifaniya, cikin watanni 6 na farkon shekararnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + sixteen =