Hukumar NIA ta musanta rike fasfunan Zakzaky da matarsa

48
Ibrahim El-Zakzaky

Hukumar leken asiri ta kasa (NIA) ta musanta cewa tana rike da fasfunan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenat.

Hakan na kunshe ne cikin sakon martanin hukumar zuwa ga malamin da matarsa, dangane da wasikarsu ta neman fasfunansu domin tafiya ganin likita zuwa kasar waje.

Malamin da matarsa, ta bakin lauyoyinsu, karkashin jagorancin Femi Falana, wani kwararren lauya, sun bayyana cewa hukumar ta rike musu fasfunansu, lokacin da jami’an tsaro, ciki har da na hukumar, suka raka su zuwa ganin likita a India, kamar yadda kotu ta bayar da umarni a shekarar 2019.

A cikin wasikar da aka aikawa hukumar, daya daga cikin lauyoyin, Abubakar Marshal, ya bukaci hukumar da ta mayarwa da malamin da matarsa fasfunansu da sauran takardun tafiye-tafiye, kasancewar yanzu an kawo karshen shari’ar da ake yi musu a babbar kotun jihar Kaduna.

Amma a martaninta cikin kakkausar murya, hukumar tace bata rike da fasfon malamin da na matarsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 9 =