Gwamnatin Jihar Kaduna a yau ta roki mutanen jihar da su kauracewa yunkurin daukar fansar kashe-kashe.
An samu yawaitar kashe-kashen mutane da na ramuwar gayya cikin watannin da suka gabata a jihar, lamarin da hukumomin tsaro suka kasa dakilewa.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya nakalto mai rike da mukamin gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe na yin rokon.
A cikin wata sanarwa da aka fitar jiya, Samuel Aruwan yace rokon ya biyo bayan kisan mutane 3 a yankin karamar hukumar Zangon Kataf a jihar.
Yace an bayar da rahoton kisan mutane ukun a wani hari na wasu mutane da ba a gano ko su waye ba, wadanda suka mamaye wasu kauyuka a yankin karamar hukumar Zangon Kataf.
Samuel Aruwan yace an raunata mazauna kauyukan su 4 yayin da aka lalata wata mota 1 da gidaje uku da bukkoki 8.
A wani labarin kuma, dakarun operation safe haven a jiya sun ceto wasu matafiya 15 da ‘yan fashin daji suka sace a kauyen Jagindi, dake karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, yace an sace mutane 15 daga cikin motaci 2 a yankin yayin da suke tafiya.
Samuel Aruwan yace sojoji sun mayar da martani bayan kiran daukin gaggawa, inda suka tura dakaru zuwa wajen.
A cewar Samuel Aruwan, mai rike da kujerar gwamnan Kaduna, Hadiza Balarabe, ta godewa sojojin bisa daukin gaggawar da suka kai, wanda ya haifar da ceto matafiyan.