Buhari ya sake nada Oloyede a JAMB, Rasheed a NUC da Bobboyi a UBEC

94

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da sake nadin shugaban hukumar jarabawar JAMB Farfesa Ishaq Olanrewaju Oloyede da shugaban hukumar kula da jami’o’i na kasa (NUC), Farfesa Abubakar Adamu Rasheed.

Wannan ya biyo bayan shawarar da ministan Ilimi, Adamu Adamu ya bai wa shugaban kasa.

An nada su ne na tsawon shekaru biyar, kuma nadin zai fara aiki tun daga ranar 1 ga watan Agustan da muke ciki.

Haka kuma shugaban kasar ya sake nada Dr Hamid Bobboyi shugaban hukumar ilimin bai daya (UBEC) a wa’adi na biyu na tsawon shekaru hudu.

Hakan na kunshe ne cikin watan sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi Ben Bem Goong ya fitar.

Sanarwar ta kuma tabbatar da Ifeoma Isiugo-Abanihe a matsayin magatakarda kuma babbar jami’ar hukumar shirya jarrabawar NABTEB.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × three =