Buhari ya jagoranci zaman majalisar tsaro ta kasa

52

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani muhimmin taro na tsaro tare da dukkan manyan hafsoshin tsaron kasarNAN da ministocin da abin ya shafa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya rawaito cewa an kira taron ne don yin nazari sosai kan kalubalen tsaro da ke addabar kasarnan da nufin samar da makoma mafi dacewa.

An bayar da rahoton cewa jami’an tsaron kasarnan, a ‘yan kwanakinan nan, suna fatattakar masu tayar da kayar baya da ‘yan fashin daji, da duk wasu masu aikata laifuka da ke damun kasarnan.

Wadanda suka halarci taron na yau sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da sakataren gwamnatin tarayya da ministocin tsaro, shari’a, harkokin cikin gida, ‘yan sanda da harkokin waje da kuma mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa.

Sauran sun hada da manyan hafsoshin tsaro karkashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro da Sufeto Janar na ‘yan sanda, da Darakta Janar na Hukumar DSS da na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Shugaban Hukumar Leken Asirin Tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − thirteen =