‘Yan Majalisa sun yi watsi da yunkurin sanya Bauchi cikin jihoshi masu man fetur

53

Majalisar Wakilai a yau tayi facali da kudirin ayyana jihar Bauchi a matsayin jiha mai samar da man fetur.

Wani dan majalisar da ya fito daga jihar ta Bauchi, Yakubu Abdullahi, ya gabatar da kudirin domin gwamnatin tarayya ta ayyana jihar a matsayin mai samar da man fetur kuma a shigar da ita cikin masu cin gajiyar kashi 13 cikin 100 na kudaden da ake samu ta man fetur.

Yakubu Abdullahi ya sanar da cewa an fara aikin hakar mai a jihar Bauchi a shekarar 2018 kuma har zuwa yanzu ana cigaba da aikin amma babu wani bayani a hukumance dangane da nasarar aikin ko akasin haka.

Yakubu Abdullahi ya roki majalisar ta umarci kwamitin albarkatun man fetur ya gayyaci kamfanin mai na kasa NNPC domin bayar da cikakken bahasi dangane da aikin da ake gudanarwa na hakar man fetur a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi da kuma nasarorin da aka samu.

Ba a yi muhawara akan kudirin ba amma da kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya nemi a kada kuri’a, wadanda basu amince ba sun samu rinjaye.

A wani labarin kuma, zauren majalisar ya kaure da hayaniya bayan da wasu ‘yan majalisar suka nuna rashin amincewa da rage kason da aka aminta a baiwa yankunan da ake tatso danyen mai.

Da farko majalisar wakilan ta amince da bai wa yankunan kaso 5 cikin 100 kamar yadda dokar PIB ta tanada amma majalisar dattawa ta rage shi zuwa kaso 3 cikin 100.

Hayaniyar ta cigaba har zuwa lokacin shigowar kakakin majalisar ta wakilai, Femi Gbajabiamila, kuma ganin haka ya sa shugaban ya bukaci shugabannin majalisar su yi ganawar sirri kan batun.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − 13 =