ME YA HANA KWANKWASO KOMAWA JAM’IYYAR APC A KARO NA BIYU ?

152
Rabiu Kwankwaso

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

Jita-Jita Mai Ƙamshin Gaskiya Ta Yaɗu A Ƴan Kanakin nan Ana Raɗe-Raɗin Kwankwaso Zai Sake Yin Hijirar Siyasa Daga PDP Zuwa APC.
-Ina Gaskiyar Wannan Batu, Wane Dalili Ne Ya Hana Hakan Faruwa A Wannan Lokaci ?
-Shin Da Gaske Kwankwaso Ya Na Shirye-Shiryen Kafa Sabuwar Jam’iyya Idan Tura Ta Kai Bango Kafin 2023 ?

Jam’iyyar APC ta baza komarta ta na cigaba da ƙoƙarin kamewa manyan jiga-jigan ƴan siyasar wannan ƙasa su dawo cikinta domin tunkarar babban zaɓen 2023 tare da fatan yin zamani mai tsawo ta na mulki a kowane mataki. Tsohon Minista, tsohon gwamna, Sanata mai ci, Eng. Rabi’u Musa Kwankwaso ya na ɗaya daga cikin manyan ƴaƴan jam’iyyar PDP waɗanda jam’iyyar ta APC ta yi wa tayin komawa cikinta.

A ƴan kwanakin da su ka gabata, jita-jita ta yi ƙarfi a shafukan sada zumunta ana raɗe-raɗi kan wannan batu. Sai dai bincike daga majiya mai toshe ya tabbatar da cewa ba shakka akwai ƙamshin gaskiya cikin jita-jitar domin da an yi nasarar yi wa Kwankwaso alƙawarin cika masa buƙatun da ya gabatarwa jam’iyyar kafin ya koma to da tuni wani zancen ma ake ba wannan ba. Wato da Kwankwaso ya ma daɗe da barin PDPn ya koma APCn a ƴan kwanakin nan kamar yadda ake raɗe-raɗi.

Kamar yadda kowa ya sani, ƴan siyasa ba sa sauya jam’iyya sai har sun cimma matsaya da jam’iyyar da za su koma kan cewa za su gabatar da buƙatun da su ke so a cika musu sannan an yi alƙawarin za a cika musun kafin su tattara kayansu su koma. 

Majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa Irin wannan tattaunawa ta gudana a tsakanin Kwankwason da uwar jam’iyyar APC ta ƙasa, Kwankwaso ya nemi a yi masa alƙawarin za a ba shi kujerar minista guda biyu, shi zai hau kan ɗaya, ya ɗora wani a kan ɗayar daga ɗaya daga cikin Jihohin wannan ƙasa. Sannan ya nemi a ba shi damar iko da kashi 50 cikin ɗari na shugabancin jam’iyyar ta APC a Jiharsa ta Kano. Waɗannan buƙatu su ne za a cika masa kafin ya koma.

Sai dai kuma jam’iyyar ta APC ba ta yarje masa akan waɗannan baƙatu ba hakan ne kuma ya hana Kwankwason gamsuwar komawa APC ɗin a karo na biyu. Da ace APCn ta yarda da waɗannan buƙatun nasa to da yanzu ƙila shirye-shiryen gabatar da gangamin taron wankansa ake kamar yadda majiya mai ƙarfi ta shaida min.

Duk da haka a iya cewa har yanzu da sauran fata a tsakanin ɓangarorin biyu duba da cewar akwai sauran lokaci kafin zaɓen 2023, kowane ɓangare ya na da buƙatar kowa domin cimma manufar siyasa nan gaba. Idan har ta tabbata aka cimma matsayar, to haƙiƙa mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje za a iya cewa ya na cikin tsaka mai wuya da ƙalubale. Domin idan Kwankwaso ya samu iko da shugabancin jam’iyya kaso 50 cikin ɗari a Jihar Kano ba raba ɗaya biyu sai ya yi duk abin da zai yi wajen ganin ya murƙushe aminin nasa, sannan babban abokin gabarsa a siyasa Ganduje domin a yanzu ba shi da burin da ya wuce wannan a siyasar.

Sanin kowa ne gwamna Ganduje a kewaye ya ke da maƙiya a cikin gwamnatinsa da bayanta waɗanda su ke nuna masa soyayyar ƙarya amma ta ƙarƙashin ƙasa da za su samu dama sai sun yaƙe shi, wasu ma daga cika yaƙar tasa su ke. Sannan akwai wasu da dama waɗanda su na cikin jam’iyyar amma su na gefe su na adawa da shi. 

Wasu ƙila saboda an ɓata musu ko an ɓatawa iyayen gidansu a gwamnatin, wasu kuma saboda sun yi wahala amma an yi watsi da su babu wani sakamako, waɗanda wasu har ma binsu ake da bitadaƙulli. Ire-iren waɗannan mutane ko shakka babu Kwankwaso zai jawo su ko kuma su ne ma da kansu za su koma wurin nasa domin su haɗa ƙarfi da ƙarfe su yaƙi Gandujen duba da ƙarfin tasirin Kwankwason da yawan mabiya.

Idan har aka kai ga rashin cimma matsaya game da komawar Kwankaso APCn kuwa hasashe na nuni da cewa Kwankwaso na ƙoƙarin haɗa kai da wasu jiga-jigan ƴan siyasa na jam’iyyu daban-daban a wannan ƙasa waɗanda za su ɗinke a wuri ɗaya domin kafa sabuwar jam’iyyar siyasar da za su yaƙi APC da PDP 2023. Koma dai mine ne lokaci ne zai nuna.

El-Bash ya rubuto wannan ra’ayin nasa ne daga jihar Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + nineteen =