Majalisar Wakilai a yau ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana dokar ta baci a kan rashin aikin yi saboda karuwar rashin tsaro a kasarnan.
Hakan yazo ne bayan an amincewa da shawarar kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, dangane da bibiyar rahotannin majalisar akan taron kasa kan tsaro.
Mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Wase, ne ya jagoranci zaman bibiyar rahotannin.
A kudirinsa, Gbajabiamila, yace za a gudanar da taron domin musayar bayanai akan dakile rashin tsaro a kasarnan, inda ya kara da cewa kwamitin ya zauna da masu ruwa da tsaki da masana tsaro, inda aka samar da shawarwari.
Yace sanadiyyar hakan,an jefa kuri’a akan shawarwarin da aka bayar cikin rahotannin tare da amincewa da su.