Mahara sun sake sace wani sarki a Kaduna

65

An sace basaraken masarautar Jaba, a Jihar Kaduna ‘Kpop Ham’ Johanathan Danladi Gyet Maude.

Yan fashin dajin sun sace basaraken ne a jihar Nasarawa.

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya tabbatar da lamarin.

Ya kuma shaida cewa an sace Maude a yankin Panda da ke Nasarawa lokacin da ya ke kan hanyar zuwa gonarsa.

Wannan labari na zuwa ne mako biyu da sace Sarkin Kajuru na jihar ta Kaduna, Alhaji Alhassan Adamu.

An saki sarkin sa’o’i 24 da sace shi, amma dai iyalansa 13 da aka sace su tare da shi har yanzu ba a sake su ba.

Yan fashin dajin sun nemi a biya su kudin fansa har naira miliyan 200.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 + ten =