Mahara sun sace matafiya sama da 50 a Sokoto

46

Akalla matafiya 50 wasu ‘yan fashin daji dauke da makamai suka sace a jihar Sokoto.

Wadanda aka sacen na tafiya ne akan titin Sokoto zuwa Gusau a jiya, lokacin da aka sace su.

Ba a samu tabbacin adadin mutanen da aka sace a lamarin na jiya da safe, amma wani da ya shaida lamarin yace sama da mutane 50 aka sace.

Da yake tabbatar da harin ga manema labari, Janar Manaja na hukumar sufurin motoci ta Sokoto, Yahuza Chika, yace motarsu guda daya ce kadai lamarin ya rutsa da ita, yayin da sauran motocin da abin ya shafa, ba na hukumar bane.

Yace mutane biyu daga cikin motar sun tsira yayin da ‘yan fashin dajin suka tafi da sauran fasinjojin.

Sai dai, bai bayar da adadin wadanda aka sace daga motar hukumar ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + seventeen =