
Shugaban Kasar Tunisia, Kais Saied, ya kori Firayim Ministan kasar Hichem Mechichi tare da dakatar da majalisar kasar, bayan mummunar zanga-zangar da aka yi jiya a duk fadin kasar.
Fushi game da yadda gwamnati ta yiwa annobar corona rikon sakainar kashi, ya kara haifar da zaman dar-dar game da matsalar tattalin arzikin kasar da zamantakewar ta.
Shugaba Saied, wanda aka zaba a shekarar 2019, ya ba da sanarwar maye gurbin Firai-Ministan.
Magoya bayan sa sun barke da murna, amma ‘yan adawa a majalisar ba tare da bata lokaci ba sun zarge shi da yin juyin mulki. Rikici tsakanin kungiyoyin hamayya ya ci gaba a yau.
Kungiyoyin na jefar juna da duwatsu a wajen majalisar, wanda sojoji suka yi wa shinge, wadanda kuma suka hana ma’aikata shiga wasu gine-ginen gwamnati.
Kais Saied, wanda bashi da jam’iyya, ya dade yana adawa da mutumin da ya cire, Firayim Minista Hichem Mechichi.