Rundunar Sojin Najeriya ta nemi mayakan Boko Haram su mika waya

43

Rundunar sojin Najeriya ta bukaci ragowar mayakan Boko Haram da su mika wuya su rungumi zaman lafiya.

Babban kwamandan runduna ta 7 ta sojojin Nijeriya, Birgediya Janar A.A. Eyitayo ne ya yi wannan kiran a wajen wani biki da sojoji suka shiryawa ‘yan jarida jiya Lahadi a Maiduguri.

Eyitayo, wanda kuma shi ne kwamandan daya daga cikin rundunar Operation Hadin Kai, ya ce sun fatattaki mayakan a farmakin da sojoji suka kai wanda ya jefa ragowar mayakan da suka tsira cikin rudani.

Ya yi nuni da cewa sojoji basa farinciki dangane da zubar da jini, a saboda haka yana kira ga sauran mayakan su rungumi zaman lafiya su mika wuya.

Hakan a cewarsa zai bawa mayakan damar cin gajiyar shirin canja musu rayuwa da koyar da su sana’o’i domin basu damar gudanar da rayuwa mai amfani a cikin al’umma.

Eyitayo ya yabawa gudunmawar da kafafen yada labarai ke bayawar wajen yaki da masu tayar da kayar baya, inda ya hori ‘yan jarida da su wayar da kan mayaka su gane gaskiya.

A wani labarin kuma, shugaban kwamitin soji na majalisar dattawan Najeriya Sanata Ali Ndume ya ce rundunar sojin kasarnan ba ta da sauran wani uzuri da za ta gabatar na kasa magance yaki da ta’addanci.

Ali Nudme ya fadi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar albarkacin bikin Ranar Dimokradiyya ta bana, inda yake alakanta maganar tasa da karin kasafin kudi da aka gabatarwa majalisa.

A makon da ya gabata ne a wajen taron majalisar koli, aka sanar da cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kwarya-kwaryar kasafin kudi na naira biliyan 895 ga Majalisar Dokokin kasar don amincewa da shi.

An ruwaito cewa shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan yace fiye da naira biliyan 700 daga cikin biliyan 895 din, an ware su ne don magance dukkan wasu matsalolin tsaro, tare da yi wa majalisar alkwarin gaggauta amincewa da kasafin.

A sanarwar tasa, Sanata Ali Ndume ya ce kudin za su taimaka wajen yaki da ta’addanci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 4 =