MDD tace mutane 350,000 na fama da yunwa a Habasha

34

Fiye da mutane dubu 350 ne ke rayuwa cikin yanayin yunwa a Habasha, in ji wani bincike da wani shiri da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya wanda ke lura da wadatar abinci.

An gudanar da binciken ne a cikin Arewacin Tigray, inda yaki ya barke a watan Nuwamba, da yankunan makwabta na Amhara da Afar tsakanin watannin Mayu da Yuni na wannan shekarar.

Binciken ya ce, ya zuwa watan Mayun bana, mutane miliyan 5.5 na fuskantar matsanancin rashin abinci.

Binciken ya kara da cewa mai yiwuwa lamarin ya ta’azzara har zuwa watan Satumba.

Kungiyar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya da Shirin samar da Abinci na Duniya, da asusun yara na UNICEF sun yi kira da a dauki matakan gaggawa don magance matsalar.

Babban Daraktan Shirin samar da Abinci na Duniya, David Beasley ya ce akwai wurare da yawa da ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya ba za su iya shiga ba.

Gwamnatin Habasha ba ta amince da rahoton ba tukunna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − five =