
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutu domin bikin ranar demokradiyya ta bana.
Hakan yazo ne a yau cikin wata sanarwa daga babban sakataren a ma’aikatar harkokin cikin gida, Shuaib Belgore.
Ranar 12 ga watan Yuni ita ce rana mafi muhimmanci a tarihin siyasar Najeriya. Ita ce ranar da aka yi amannar cewa an gudanar da zabe mafi gaskiya da adalchi na shugaban kasa a kasarnan.
An soke sakamakon zaben inda aka kulle wanda ya kamata ya lashe zaben, Moshood Abiola.
Gwamnatin Buhari ta ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar demokradiyya, duk da kasancewar ana gudanar da sauyin mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Sanarwar tace ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, wanda ya ayyana hutun, ya taya ‘yan Najeriya murnar zuwan ranar.
Ya shawarci yan kasarnan da su marawa gwamnati mai ci baya a kokarinta na tabbatar da hadin kai da yalwar arzikin kasarnan.