Wasu da ake zargi ‘yan fashin daji ne sun kashe akalla mutane 93 a wasu hare-hare kan wasu kauyuka 6 a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Kauyukan sun hada da Kadawa da Kwata da Maduba da Ganda Samu da Saulawa da kuma Askawa.
Daruruwan mazauna kauyukan ne aka raba da gidajensu sanadiyyar hare-haren, inda dayawa daga cikinsu, da suka hada da mata da kananan yara, suke neman mafaka a garuruwan Dauran da Zurmi.
Mazauna garin sun ce wasu mutane akan babura dauke da makamai sun farwa kauyukansu inda suka fara harbi kan jama’a.
An kwashe gawarwakin mutanen da aka kashe a sabbin hare-haren inda aka kaisu zuwa garin Dauran, dake da nisan kilomita 10 yamma daga garin Zurmi, helkwatar karamar hukumar Zurmi.
Kakakin ‘yansanda na jihar, SP Muhammad Shehu, yace yansanda sun kwaso gawarwaki 14 domin a binnesu a makabartar Unguwar Gwaza dake Gusau, babban birnin jihar.
A wani labarin kuma, biyo bayan kashe-kashen mutanen da aka yi a kauyen Kadawa, Gwamna Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi, Alhaji Abubakar Muhammad.
An sanar da dakatar da sarkin cikin wata sanarwa a jiya, dauke da sa hannun mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe.
Cikin ‘yan makonninnan, an samu karuwar hare-hare a karamar hukumar Zurmi.
A makon da ya wuce, wasu fusatattun matasa suka datse hanyar Gusau zuwa Kaura-Namoda zuwa Zurmi inda suke zanga-zanga kan kashe-kashen da ake yi.
Kafin nan kuma, an taba gudanar da zanga-zanga a fadar Sarkin Zurmi.
Kazalika, gwamnatin jihar Zamfara ta soke bikin ranar demokradiyya a jihar saboda halin rashin tsaro, duk da kasancewar Gwamna Bello Matawalle ya umarci mutanen jihar da su tsare kawunansu daga hare-haren ‘yan fashin daji.
Gwamnan ya sanar da haka a jiya lokacin da yake jawabi a Gusau, babban birnin jihar, a wajen taron addu’o’in da gwamnatin jihar ta shirya domin neman daukin Allah wajen ganin bayan ‘yan fashin daji.