An tabbatar da Faruk Yahaya a matsayin babban hafsan sojin kasa

54

Majalisar Dattawa a yau ta tabbatar da nadin Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin babban hafsan sojin kasa.

Tabbatarwar ta biyo bayan aiki da rahoton kwamitin hadaka na tsaro da na sojoji, a karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko da Sanata Ali Ndume.

Shugaban kwamitin hadakar, Sanata Aliyu Wamakko, a bayaninsa yace kwamitin ya gamsu da tantancewar da aka yiwa wanda aka nada.

Ya sanar da cewa kwamitin bai samu wani korafi ba dangane da wanda aka nada kuma hukumar tsaro ta DSS ta wanke shi.

Shugaban kasa Muhammadu tun a farkon watannan, ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da Faruk Yahaya, wanda aka nada bayan rasuwar tsohon babban hafsan soji, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru.

Tsohon babban hafsan sojin ya rasu a wani hadarin jirgin sama a kusa da filin jiragen saman kasa da kasa na Kaduna a watan da ya gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 4 =