‘Yansanda sun kama ‘yan bindigan da suka kashe Gulak

27

‘Yansanda sun sanar da kama ‘yan bindigar da suka kashe Ahmed Gulak, jigo a jam’iyyar APC.

An harbe Ahmed Gulak har lahira jiya da safe a jihar Imo.

Ance direban motar da ya dauke shi zuwa filin jiragen sama ya sha tambayoyi a hannun jami’an tsaro kuma ya bayyana motocin da yan bindigar suka yi amfani da su, da suka hada da Toyota camry da Toyota sienna da Toyota hilux da kuma Lexus.

Wani rahoton halin da ake ciki ya nuna cewa kafin a kashe Ahmed Gulak, wasu mutane sun toshe titin zuwa filin jiragen sama na Imo a mahadar Obiangwu a yankin karamar hukumar Ngor-Okpala.

Sai dai, wani bai taimakawa Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo akan kafafen sadarwa na zamani, Ambrose Nwaogwugwu, ya bayyana kamen yan bindigar da cewa cigaba ne sosai a binciken da ake yi kan kisan na Ahmed Gulak.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × two =