Hukumar Sojin Najeriya ta yi kiranye ga sojojin dake karatu domin yakar boko haram

82

Biyo bayan zafafa hare-hare a fadin kasarnan, musamman a Arewa, hukumar sojin Najeriya ta dawo da adadi mai yawa na jami’anta da ke karatu a manyan makarantun fararen hula a fadin kasarnan, kamar yadda yazo a wani bayanin sirri da ya fito daga Helkwatar Sojojin Najeriya dake Abuja.

A cikin bayanin da ke dauke da kwanan watan 11 ga Mayu, hukumar sojin Nijeriya ta kuma dakatar da daukar nauyin karatun sojoji a manyan makarantun fararen hula in banda wadanda ke shekarar karshe.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da sojoji ke cigaba da rasa rayuka da dama a yakin da suke yi na fatattakar ‘yan tawaye wanda ya kuma jawo kisan daruruwan ‘yan Boko Haram da mayakan ISWAP a hannun sojojin Najeriya.

A daya daga cikin hare-haren na baya-bayan nan, an bayar da rahoton kashe sojoji sama da 30 a watan Afrilu lokacin da mayakan ISIS suka yi wa tawagar sojojin da ke rakiyar makamai kwanton-bauna tare da mamaye wani sansanin soji a Mainok, Jihar Borno.

Wata guda kafin haka, kimanin sojoji 30 aka bayar da rahoton an kashe a hare-hare hudu da mayakan suka kai a yankin Arewa maso Gabas.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + five =