Babban hafsan sojin kasa, Ibrahim Attahiru, ya rasu a hadarin jirgin sama a lokacin wata ziyarar aiki zuwa Kaduna, jaridar ya PRNigeria mai alaka da sojoji ta raiwato.
Hukumar sojin saman Najeriya ta tabbatar da aukuwar hadarin amma bata bayar da cikakken bayani ba.
PRNigeria ta raiwato cewa wasu daga cikin hadiman Ibrahim Attahiru sun mutu a hadarin.
Kwanakin baya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Attahiru a matsayin babban hasfan sojin kasa.
Har kawo lokacin da aka nada shi a watan Janairu, shine kwamadan barikin sojin Najeriya ta 82 dake Enugu.