An saki sunaye 6,105 na masu neman aikin Immigration

119

Hukumar kula da yan civil defence da ma’aikatan gidajen gyaran da’a da ‘yan kwana-kwana da ma’aikatan hukumar kula da shige da fice immigration, ta sanar da cewa an saki sunayen mutane 6,105 wadanda za a tantance domin yiwuwar daukarsu aiki a hukumar kula da shige da fice immigration.

Kakakin hukumar ta immigration, Sunday James, ya sanar da haka cikin wata sanarwa a yau.

Sunday James ya shawarci wadanda za a tuntuba ta email ko waya da su duba shafin internet na hukumar; https://immigrationrecruitment.org.ng domin karin bayani.

Sanarwar tace za a gudanar da tantancewar a kyauta kuma ana sa ran farawa a ranar 24 ga watan Mayu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 12 =