Osinbajo ya saka bajin karin mukami ga sabon shugaban yansanda

55

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya saka bajin karin mukami ga mukaddashin Sufeto Janar na Yansanda, Usman Alkali Baba.

A jiya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Alkali Baba a matsayin mukaddashin Sufeto Janar na Yansanda.

Sanarwar da ministan harkokin yansanda, Maigari Dingyadi, ya sanar, ta fara aiki nan take.

Mukaddashin Sufeto Janar na Yansanda ya maye gurbin Mohammed Adamu, wanda wa’adin mulkinsa ya kare a ranar 1 ga watan Fabrairu 2021 amma aka kara masa watanni 3.

Kafin nadinsa, Usman Baba mataimakin Sufeto Janar na Yansanda ne.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin da aka gudanar a dakin taron mataimakin shugaban kasa, sun hada da tsohon Sufeto Janar na Yansanda, Mohammed Adamu, da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − ten =