Ministan wutar lantarki ya nemi afuwa saboda rashin wuta

49

Ministan wutar lantarki, Sale Mamman, a yau ya nemi afuwa dangane da rashin wutar lantarki da yan Najeriya da dama ke fuskanta a fadin kasarnan.

A cewarsa, matsalar ta samo asaline sanadiyyar lalacewar wasu injinan samar da wutar lantarki.

Sale Mamman, wanda ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter, sai dai, ya tabbatarwa da yan Najeriya cewa za a gyara matsalar kuma a dawo da wuta.

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta soke zaman ganawar da ta shirya gudanarwa a yau tsakaninta da malaman polytechnic da ma’aikatan kotuna da ke yajin aiki.

Ba a bayar da dalilin soke zaman ganawar ba, wanda aka shirya da nufin sanya malaman makarantun kimiyya da fasahar da ma’aikatan kotunan su janye yajin aikin da suke yi na sai baba ta gani.

Kakakin ma’ikatar kwadago da aikin yi, Charles Akpan, ya tabbatar da cewa an soke zaman ganawar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − five =